Hukumar Za?e ta ?asa (INEC) ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da wani labari da ake ya?awa wai ta na ?aukar mutane aiki.
Mista Festus Okoye, Babban Kwamishina kuma Shugaban Ya?a Labarai da Wayar da kan Masu Za?e na hukumar, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Juma’a a Abuja.
Okoye ya ce a yanzu dai INEC ba ta ?aukar kowa aiki, ya ?ara da cewa tun tuni aka dakatar da ?aukar sabbin gama jami’a da ?wararrun ma’aikata.
Ya ce: “INEC na so ta ?ara jawo hankalin jama’a zuwa ga aikin da wasu jami’an ?arya ‘yan damfara su ke yi na ?aukar aiki na jabu.
“’Yan damfarar sun bu?e gidajen yana na ?aryar ?aukar aiki inda su ke kar?ar ku?a?e a hannun jama’ar da ba su ankara ba har su na ba su takardun kama aiki na bogi da sunan Hukumar.
“Idan za a iya tunawa, tun a ranar 30 ga Mayu, 2020, Hukumar ta bada wata sanarwa inda ta ja hankalin jama’a kan ya?uwar wasu takardun kama aiki na ?arya da aka ce wai sun fito daga gare ta ne.
“Mun sanar da jama’a lokacin cewa Hukumar ta dakatar da shirin ta na ?aukar ma’aikata.
“Mun shawarci kowa da kowa da ya yi watsi da duk wata ji-ta-ji-ta game da ?aukar aiki da raba takardun kama aiki da aka ce wai daga Hukumar ne su ka fito, kuma mun sanar da hukumomin tsaro wannan damfarar.”
Okoye ya ce wannan Hukuma dai amanar jama’a ce wadda ke gudanar da aikin ta a bisa tsarin da aka amince da shi na aiki tsakani da Allah kuma a bayyane.
Ya ce wannan tsari na yin aiki a bayyane shi ya sanya a duk lokacin da hukumar ke ?aukar ma’aika ake yayatawa.
Okoye ya ce, “Mu an ?ara jan hankalin jama’a da su san dabarun da ‘yan damfara ke amfani da su don kada su fa?a cikin tarkon su na masu aikata laifi.”