Babu Gaskiya A Labarin Katse Hanyoyin Sadarwa A Kaduna – El Rufa’i

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta wata jita-jita da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa gwamnatin jihar na shirin katse sadarwa a jihar don yaki da ‘yan bindiga kamar yadda aka yi a jihar Zamfara.

Wata sanarwar mai ba wa gwamnan jihar shawara kan harkokin watsa labarai Muyiwa Adekeye, gwamnatin ta bayyana cewa bata tuntubi kowacce hukuma ta gwamnatin ?asar da zummar neman a katse layuna sadarwa ba, don haka jama’a su yi watsi da batun.

”Zance ne mara tushe ballantana makama, babu wannan batu a jihar Kaduna, a bayyana muke komai da ya shafi tsaro, idan akwai wannan bukata za mu dauki matakin da ya dace.

Jihar Kaduna dai na cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, kuma yayin da gwamnatin Zamfara ta katse layukan sadarwa, ana ganin suma sauran jihohin da ke ma?otaka da ita da ke fama da wannan matsala za su dauki irin wannan mataki nan gaba wata?ila

Related posts

Leave a Comment