Babu Gaskiya A Labarin Kai Wa Ayarin Tinubu Hari – ‘Yan Sanda

Rundunar yan sanda reshen jihar Osun ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta cewa an farmaki Ayarin ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu a ƙarshen makon nan a babban birnin Jihar.

An ruwaito cewa rundunar ta musanta jita-jitar ne a wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola, ya fitar wadda aka rarraba ta ga manema labarai a jihar.

Ya bayyana cewa labarin da Bidiyon da ake yaɗa wa ake jingina shi ga Ayarin Tinubu ba na yanzu bane, farmaki ne da aka kaiwa ayarin gwamna Oyetola lokacin zanga-zangar EndSARS a watan Oktoban shekarar 2020.

“An jawo hankalin hukumar ‘yan sanda kan wani labari da Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta mai nuna cewa matasan Osun sun farmaki ayarin Sanata Bola Tinubu ranar 8 ga watan Oktoba, 2022.” “Hukumar yan sanda na sanar da ɗaukacin al’umma cewa labarin da Bidiyon wani hari ne da aka kai wa Ayarin gwamnan Osun, Oyetola Adegboyega, lokacin zanga-zangar EndSARS shekara biyu da suka gabata, 17 ga Oktoba, 2022.”

“Kwamishinan ‘yan sanda, Olawale Olokode, na sanar wa mutane cewa labarin ba haka yake ba kuma ya saɓa, wanda wasu gurbatattun mutane ke yaɗa shi da nufin ta da hankula.” Tinubu bai ziyarci jihar Osun ba kwanan nan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply