Babu Gaskiya A Labarin Dasa Bama-Bamai A Abuja – ‘Yan Sanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumar yan sandan Najeriya ta yi watsi da labaran cewa an dasa bama-bamai a wasu wurare dake birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Hukumar ta ce karya ne kuma da ban mamaki wasu da ake yiwa kallon mutanen kirki ke yada wannan labari mara tushe ballantana makama.

Hakan na kunshe cikin jawabin da Kakakin hukumar yan sandan kasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba kuma aka rarraba wa manema labarai a Abuja.

“Ban tunanin zamu yiwa kasarmu adalci idan muka cigaba da yada labarun karya don tada hankulan mutane da mazauna birnin tarayya da Najeriya gaba daya.” “Da ban mamaki da ban haushi ka karanta a labarai a soshiyar midiya cewa an dasa bama-bamai a dukkan unguwannin Abuja, har daga bakin wasu da ake yiwa kallon jakadun zaman lafiya.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply