Babu Gaskiya A Labarin Cire Kakakin Tinubu Daga Kwamitin Zabe – Fadar Shugaban Kasa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya musanta rahotannin da ke cewa ya bukaci Bola Tinubu, ya cire Festus Keyamo daga mukamin kakakin kwamitin yakin neman zabensa.

A wata sanarwa Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaba Buhari ya walafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin, ya ce rahotannin da ke cewa shugaban kasar yana so a cire Keyamo daga kwamitin “karya ne.”

“Shugaba Buhari da dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu suna farin cikin aikin da Keyamo yake yi, da kuma yadda aka tsara gudanar da yakin neman zabe, wanda ya zama abin koyi ga sauran jam’iyyu,” in ji sanarwar.

Garba Shehu ya kara da cewa suna sane da makircin da ake kitsawa domin bata shugabannin jam’iyyarsu da kuma yi wa yakin neman zabensu tarnaki.

Ya bukaci masu goyon bayan jam’iyyar APC da su daina ba da muhimmanci ga labaran karya da ake watsawa kan shugabanninsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply