Babu Dalilin Zanga-Zanga, Mun Magance Da Yawa Daga Cikin Bukatun Masu Zanga-Zangar – Fadar Shugaban Kasa

IMG 20240225 WA0030

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu babu bukatar yin zanga-zanga domin tuni ta fara tinkarar bukatun ‘yan Najeriya da ke ci gaba da kokawa.

Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a Yau Litinin Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, “Ana magance da yawa daga cikin batutuwan da masu shirya zanga-zangar suke tadawa, gwamnati na kokarin ganin an samar da abinci. .”

“An raba shinkafar zuwa cibiyoyi daban-daban a fadin kasar nan, ana kuma sayar da ita a kan Naira 40,000. Wannan mafari ne kuma matakin farko da ya zama dole, ana kuma ci gaba da kokarin”.

“Akwai manyan saka hannun jari a fannin noma, kuma mun yi imanin cewa yayin da muke ci gaba, farashin kayan abinci zai ragu.”

Ministan ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya yi imanin gwamnati na magance matsalolin da matasa ke fuskanta, inda ya kara da cewa, “Shirin rancen dalibai ya tabbatar da cewa ba za a bar wani matashin da ke son zuwa makaranta ba, da zarar an gama aiwatar da shirin na CNG, matsalar sufuri za ta kasance. a warware.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply