Babu Dalilin Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Gwamnan Kogi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, yace gwamnatinsa ba za ta taba sasanci ko yin wani zaman sulhu da ‘yan ta’adda ba, domin ?ata lokaci ne kuma babu dalilin yin hakan.

Yahaya Bello ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin siyasarmu a yau, akan matsalar tsaro da ta da?e tana addabar Najeriya musamman yankin Arewacin Kasar.

Gwamnan Yahaya Bello ya cigaba da cewar, babu wani cigaban azo a gani da aka samu a Jihohin da gwamnonin su suka gudanar da sulhu da ‘yan bindiga, sai dai kawai ‘yan Bindigar sun mayar da harkar ce a matsayin wata hanya ta samun ku?i.

“Bana goyon bayan sulhu da ‘yan ta’adda kuma ba zan goyi bayan shirin ba saboda bai da wani amfani, sai dai ?ara yamutsa abubuwa da yake yi”.

Bisa ga wadannan kalamai na Yahaya Bello akan ‘yan bindiga ya zama Gwamna na biyu kenan daga yankin Arewa bayan gwamna Nasiru El Rufa’i na wanda bai goyi bayan matakin sulhu da ‘yan ta’adda ba.

Related posts

Leave a Comment