Ministan yada labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammad ya mayarwa PDP martani akan kiran da takewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sauka daga Mulki.
Mista Lai ya bayyana hakan ne a ganawar da ya yi da manema labarai, inda ya kara da cewa shugaban kasar ya yi kokari a yaki da rashawa da yake domin zuwa yanzu ya kwato kudi sama Naira Biliyan 800.
Yace kiran da PDP take cewa shugaban kasar ya sauka shirmene kawai. Kuma binciken rashawa da ake a wasu ma’aikatun gwamnati, hakan na nuna cewa shugaban na aiki yanda ya kamata.