An bayyana cewar babu dalilin gudanar da bikin tunawa da Marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello da Shugabannin ke yi a yanzu matu?ar ba za suyi koyi da halayen kwarai na Marigayin ba.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar APC ta jihar Kaduna mai suna Alhaji Abdullahi Gambo Abba, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna dangane da zagoyawar rasuwar Sardaunan Sokoto da wasu manya ‘yan Mazan jiya shekaru 55 a Kaduna.
Gambo Abba ya ?ara da cewar ba komai ya sanya ake cigaba da bikin tunawa da Sardauna ba tsawon lokaci, sai ayyukan alheri da ya gabatar a lokacin rayuwarshi, saboda haka wannan babban kalubale ne ga shugabannin a yanzu da su aikata ayyuka nagari yadda su ma za’a cigaba da tunawa da su bayan shudewarsu.
?an siyasar wanda ke rike da Sarautar gargajiya ta Jakadan Hayin Banki Kaduna, ya yi tsokaci dangane da halin da kasa ta shiga a halin yanzu na ta?ar?arewar tsaro, inda yace a magana ta gaskiya gwamnati ta gaza ta wannan fannin, kuma lallai babban kalubale ne gareta da ta tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya kamar yadda ta yi al?awari.