Babu Barazanar Tsaro A Abuja – Baturen ‘Yan Sanda

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya IGP Usman Alkali Baba ya jaddada cewa babu wata fargabar kai hare-hare a Abuja babban birnin ƙasar.

A ranar Lahadi ne Amurka da Birtaniya suka gargaɗi ‘yan ƙasashensu cewa ‘yan ta’adda na shirin kai hare-hare a birnin, inda suka shawarce su da su ankare. Sauran ƙasashe kamar Jamus da Australiya da Kanada da Ireland duk sun bayyana fargabar kai hari a birnin.

A ranar Juma’a kuma Amurka ta umarci jami’an diflomasiyyarta da iyalansu su gaggauta ficewa daga Abujar sakamakon fargabar da ake da ita ta kai harin ta’addanci.

Cikin wata sanarwa daga kakakin ‘yan sandan Najeeriya Olumuyiwa Adejobi ya fitar ranar Alhamis, IGP Alkali ya tabbatar wa ‘yan ƙasar wajen da ma mazauna Abuja game da tsaron lafiyarsu, yana mai umartar jami’ansa da su tsaurara tsaro a kewayen Abuja.

“Saboda haka IGP na kwantar wa da mazauna Abuja hankali tare da ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum yayin da aka shirya tsafi don daƙile barazanar tsaro da kuma amsa kiran gaggawa a kan lokaci,” in ji sanarwar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply