Babbar Sallah: Buhari Ya Kalubalanci Musulmi Da Sanya Najeriya A Addu’a

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi kira ga jama’ar musulmi da su yi amfani da lokacin bukukuwan babbar Sallah wajen sanya Najeriya cikin addu’a.

Shugaban ya yi kiran ne a sakon barka da Sallah da ya aike wa jama’ar Najeriya a safiyar ranar babbar sallar bana.

“Matu?ar jama’a za su rinka bin tsari da karantarwar addini babu shakka miyagun ayyuka da ke faruwa a kasar za su yi sauki.

Shugaban ya ?ara da cewar yana sane da irin halin da ‘yan Najeriya ke ciki na ?unci da rashin tsaro, inda ya bada tabbacin daidaita al’amura kafin karewar wa’adin mulkinsa.

Related posts

Leave a Comment