Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Usaini Gumel, ya gargaɗi dukkan DPO na ‘yan sandan Jihar Kano a ƙananan hukumomi 44, cewa su daina tsare wanda ake zargi da laifi fiye da kwanaki biyu, wato sa’o’i 48, ba tare da sun bada beli ko sun gabatar da mutum kotu ba.
Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa Gumel ya yi wannan gargaɗin yayin da ya kai ziyarar rangadin wasu dibijin-dibijin na cikin birnin Kano.
Ya ce tsare wanda ake zargi fiye da sa’o’i 24 ba tare da kai shi kotu ba, tauyewa ce da danne masa ‘yanci, saboda duk wanda ‘yan sanda suka tsare, ba za a ce mai laifi ba ne, har sai kotu ta tabbatar da laifin a kan sa.
Kwamishinan ‘Yan Sanda Gumel ya kuma tunatar da DPO ɗin cewa kyauta ake bayar da beli, ba tare da karɓar ko sisi daga hannun mai beli ba.
Daga nan ya ƙara gargaɗin su su riƙa kiyayewa da ‘yancin wanda su ke tsarewa, kuma su guji aikata duk abin da zai iya taɓa lafiyar wanda ke tsare a hannun su.
A yayin rangadin, Gumel ya samu rakiyar wakilan Hukumar Gidan Kurkukun Kano, Hukumar Kare Haƙƙin Jama’a, Ofishin Antoni Janar na Jiha da kuma wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin jama’a.
Ya ce ziyarar-bazatar da ya kai wasu rassan DPO ɗin a cikin Kano, ta na kan tsarin PDSS wanda aka ƙaddamar cikin watan Disamba, 2023.
“Dukkan ba’arin mutane na so su ga cewa su na samun adalci a hannun ‘yan sanda.
“Saboda haka akwai umarni da gargaɗi daga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda na Najeriya, zuwa ga dukkan Kwashinonin ‘Yan Sanda na faɗin ƙasar nan cewa, su tabbatar su na kiyaye cin zarafin waɗanda ke tsare, domin su ma su na da ‘yancin su na ‘yan Adam.
Kuma ya ce tilas duk wanda ‘yan sanda suka maka kotu, to a riƙa samo masa lauya, wanda zai riƙa tsaya masu a kotuna.
“Mun je Ofishin DOP na Zango, Fagge, Sharaɗa da Gidan Kurkuku na Janguza. Mun yi zagayen gani da ido, inda a Kurkukun Janguza muka ga har kotun zartas da shari’u na sammacin ke cikin kurkukun.