Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Babban Kuskure Ne Afuwar Da Gwamnati Ke Yi Wa ‘Yan Boko Haram – Majalisa

Majalisar Dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ?ar?ashin jagorancin Shugaban ?asa Muhammadu Buhari da cewar ta yi koyi da takwararta Ha?a??iyar daular Larabawa, UAE, wajen za?ulo masu ?aukar nauyin Boko Haram a Najeriya don ?aukar matakin ladabtarwa da gaggawa.

Sanatocin sun kuma yi kira ga rundunar sojin Najeriya da ta tayi watsi da bawa tubabbun ?an Boko Haram kariya wa?anda suke da hannu dumu dumu wajen kisan kiyashi da lalata dukiyar al-umma,inda suka ce tsarin kwata kwata ba dai-dai bane.

Da yake magana da ?an jaridu jim ka?an bayan ganawar sirri da shugaban rundunar Soji, Janaral Yusuf Buratai akan shawarwarin kasafin ku?in tsaro na shekarar 2021,shugaban kwamitin Sanatoci akan rundunar Soji, Sanata Ali Ndume, ya ce ?asar ha?a??iyar Daular Larabawa ta yi aiki mai kyau, abin koyi.

A farkon makon nan ne kasar Daular Larabawan ta ?aure wa?anda ake zargi da ?aukar nauyin Boko Haram, inda yace ana jan ciki wajen yankewa masu irin wannan laifi hukunci a Najeriya.

Ya ?ara da cewa ba tubabbun ?an Boko Haram kariya na iya kawo na?asu a ya?in da ake da ta’addanci.

“Muna yabawa gwamnatin ha?a??iyar Daular Larabawa kuma har yanzu muna ro?on gwamnatin mu kan ta za?ulo masu ?aukar nauyin ?ungiyar a fili ko a ?oye don gurfanar da su gaban kuliya cikin hanzari.
“Ba mu yarda da ba tubabbun ?an Boko Haram kariya ba, Matsayar ?angaren zartarwa daban, bazai yiwu ku rin?a shagwa?a tubabbun ?an Boko Haram ba da jinda?i, su kuma wanda ayyukansu ta shafa ku barsu a sansanin ?an gudun hijira, hakan ba adalci bane.

“Har yanzu Muna kira ga gwamnatin Najeriya da ta za?ulo masu hannu a ?aukar nauyin Boko Haram a zahirance ko a ba?ini don yin misali akansu don ya zama izina ga masu aikata ta’addanci.

“Ban yarda da gwamnatin Najeriya ba akan sauyawa tubabbun ?an ?ungiyar suna da kuma yafe musu laifukansu, saboda basu cancanci hakan ba. “Ba zai yiwu ba ace kura da shan bugu gardi da ?wace ku?i, su ne da laifi kuma sune da jinda?i, inda su kuma wa?anda abin ya shafa ko oho.

Na yarda cewa dani da sauran ?an Najeriya masu yawa matsayar mu ?aya.”

Exit mobile version