Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya isa jihar Kaduna a karon farko bayan tube masa rawani a watanni biyar da suka gabata.
Dubban masoya da masu fatan alheri ga tsohon sarkin Kanon sun fito da safiyar Lahadi inda suka yi cincirindo don masa barka da zuwa.
Tsohon Sarki Sanusi ya ziyarci jihar Kaduna a daidai lokacin bikin murnar cikar gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, shekaru 60 a duniya.
A lokacin da aka tube rawanin basaraken a ranar 9 ga watan Maris na 2020, El-Rufai ya nada Sanusi a matsayin shugaban jami’ar jihar Kaduna kuma mataimakin shugaban majalisar karfafa kasuwanci ta jihar.
Babban mataimaki na musamman ga basaraken, Dr Suleiman Shinkafi, ya ce tsohon sarkin zai kwashe mako daya a birnin Kaduna inda zai dinga karbar bakin da ke son ganinsa.
“Tun bayan tube masa rawani, jama’a da yawa sun nuna bukatar son kai masa ziyara a Legas. Amma basaraken ya yanke hukuncin saukake musu wahalar zuwa har jihar Legas ganinsa,”
Shinkafi ya kara da cewa, basaraken zai ziyarci jihar Sokoto inda zai mika gaisuwa ga Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad, kafin ya karasa Azare da ke karamar hukumar Katagum ta jihar Bauchi.
A nan ne kakansa Muhammadu Sanusi I ya zauna bayan marigayi Sardaunan Sokoto , Ahmadu Bello ya tube masa rawani. Sanusi, wanda ya sauka a barikin sojin saman Najeriya wurin karfe 10:40 na safe, ya sauka daga jirgi inda a take matansa suka biyo baya.
Wasu masu sarauta a Kano da Kaduna duk sun hallara a barikin dakarun sojin saman Najeriyan don karbar bakuncinsa. Babu bata lokaci basaraken ya shiga motar alfarma wacce ke jiransa inda aka rankaya da shi gidan gwamnatin jihar Kaduna don ganawa da Gwamna Nasir El-Rufai.
Sanusi tsohon shugaban babban bankin Najeriya ne wanda alakarsu ta yi tsami da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano tun a shekarar 2017. Magoya bayansa sun yarda cewa, rashin nuna goyon baya ga tazarcen Gwamna Ganduje ce daya daga cikin dalilan da suka sa aka tube masa rawani.