Babban Burina Shine Tsamar Da ‘Yan Najeriya Miliyan 100 Daga Talauci – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya ce ya na nan ya na kokarin cika muradin sa na ganin ya ceto mutum milyan 100 daga fatara da talauci. Ya kuma ce ko masu hassada sun san cewa gwamnatin sa ta yi rawar gani a cikin wannan shekara daya, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Buhari ya yi wannan bayani ne daidai lokacin da rashin aikin yi ke kara dumfarar ƴan Najeriya da dama, ƙarin kuɗin fetur, ƙarin kuɗin wutar lantarki da kuma hauhawar farashin abincin da talakawa ke yi, wanda a yanzu ke neman ya gagare su.

Wannan bayani Buhari ya yi shi a wurin rufe taron Sanin-makamar-aiki da aka shirya wa Ministoci, Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya da sauran manyan jami’an gwamnati.

Labarai Makamanta

Leave a Reply