Babban Bankin Najeriya Ya Raba Tallafin Bashin Noma A Neja

A ƙoƙarin bunƙasa harkar noma a Najeriya. Babban bankin ƙasa (CBN) haɗin guiwa da gwamnatin Jihar, ta raba tallafin bashin kayan noma ga manoman shinkafa sama da ɗari biyar a garin Kontagora dake Jihar Neja. Bashin kayan noman waɗanda suka haɗa ba, buhun shinkafa, buhunan takin zamani, maganin feshi, injimin ban ruwa, injimin feshi. Domin bunƙasa harkar noman shinkafa a cikin ƙasa.

Ƙaddamarwar wanda ya gudana a jiya alhamis ƙarƙashin jagorancin babban bankin Najeriya, da wakilcin Ƙungiyar manoma shinkafa ta ƙasa (RIFAN) da wakilin shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar Neja Alhaji Balarabe Kagara, wanda Alhaji Abubakar Ɗan Usman (Sarkin Bakin Kontagora) ya wakilta.

Tallafin bashin wanda manomar zasu biya cikin shekaru uku, an kuma yi kira ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin da suyi anfani dashi kamar yadda ya dace domin anfanar kan su da al’umma.

Dadaman waɗanda suka samu tallafin ne suka bayyana godiyar su, tare da shan alwashin yin anfani dashi domin bunƙasa harkar noma a Najeriya. Wanda zai taimaka wurin habbaka tattalin arzikin ƙasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply