Babban Banki Bai Buga Sabbin Kudi Ba Fenti Aka Yi Wa Tsofaffi – Gudaji Kazaure

Ɗan Majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Kazaure da Gwiwa a Jihar Jigawa Honorabul Gudaji Kazaure, ya fito fili ya kalubalanci buga sabbin takardun naira da CBN ke ikirarin yi inda yace karya ne ba a buga sabbi ba fenti kawai aka yi wa tsofaffin.

Gudaji Kazaure ya kwarmata wannan magana a tattaunawar da gidan rediyon DW ya yi dashi akan cece kuce da ake yi akan sabbin takardun kuɗin da bankin ya buga.

Ɗan Majalisar ya ƙara da cewar a matsayin shi na kwararre wanda ya san yadda ake buga takardu, yana da tabbacin cewa CBN bai buga sabbin takardun kudi ba kawai kwaskwarima aka yi wa tsofaffin ta hanyar yi musu fenti.

“Ga dukkanin mai hankali idan ya kalli waɗannan sabbin takardun Naira da ake magana sannan ya kwatanta da tsoffin da ake dasu zai ga babu wani bambanci akai sai fenti da aka yi, kuma tabbas idan aka rina tsoffin da shudin launi babu makawa za su koma wadannan sabbi da ake magana akai”.

Gudaji Kazaure ya ƙara da cewar wannan shi ya sanya CBN ya yi wayo da dabarar cewa komai yawan kudin da mutum ya kai banki ba za a musanya mishi da sabbi ba sai dai a buɗe mishi asusu, kuma ko ya tafi ATM ba zai cire sama da Naira 100,000 ba, wanda duk mai hankali zai gane cewa wannan karya ce da kuma yaudara domin babu sabbin da aka buga.

“Zan yi dukkanin mai yiwuwa wajen kokarin sanar da shugaban kasa wannan badakala da CBN ta yi domin ɗaukar matakin da ya dace, saboda mun gano CBN na kokarin batar da sawun binciken da Kwamitin mu ya yi ne na gano makudan Triliyoyin Naira da aka yi sama da faɗi dasu”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply