Babban Ɗan Majalisar Masarautar Zazzau Ya Ajiye Muƙami

Malam Aminu Yakubu-Wambai, ya yi murabus daga sarautarsa ta Wakilin Raya Kasar Zazzau, bayan sa’o’i kadan da nada sabon sarkin Zazzau.wakilin raya kasar Zazzau na daya daga cikin ‘yan majalisar Sarkin Zazzau.

Alhji Aminu Wanbai ya shafe shekaru 19 a masarautar zazzau a matsayin dan majalisar masarautar zazzau mai wakiltan Kaduna ta kudu. Kuma ya ajiye mukamin sa ne kawai Ba dan wata Matsala ba kamar yadda ya bayyana a wasikar ajiye mukamin sa.

Kamar yadda muka kawo maku ruhotanni a jiya laraba ne Gwamna Nasir El-Rufai ya nada Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau bayan rasuwar marigayi Dakta Shehu Idris a ranar 10 ga watan Satumba.

Ya kuke kallon wannan ajiye mukamin da wakilin raya kasar zazzau yayi musamman a wannan lokaci?

Labarai Makamanta

Leave a Reply