Babangida Shugaba Ne Nagari Da ‘Yan Najeriya Baza Su Manta Ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun ‘yan Najeriya wajen taya tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida, wanda ya cika shekaru 79 a duniya murnar zagayowar ranar haihuwa shi.

A wani sakon taya murna da kakakinsa, Femi Adesina ya saki, Buhari ya bayyana cewa a kullun ‘yan Najeriya za su dunga tuna kyawawan ayyukan tsohon shugaban kasa Babangida.

“Yayin da tsohon shugaban kasa a mulkin soja ya cika shekaru 79, Shugaban kasar ya yi amanna cewa kasar za ta dunga tunawa da ayyukansa a koda yaushe.

“Shugaba Buhari na addu’a ga Allah a kan ya ci gaba da kara wa Janar Babangida karfi, ya kara masa lafiya da tsawon rai.”

An haifi tsohon Shugaban kasa Babangida a ranar 17 ga watan Agusta, 1941 sannan ya yi shugabanci tsakanin 1985 da 1993.

Tsohon shugaban kasar ya rike mukamai a rundunar soji sannan ya yi yaki a lokacin yakin basasan Najeriya. Babangida wanda ya kasance haifafan garin Minna, jihar Neja ya shiga rundunar sojin Najeriya a ranar 10 ga watan Disamba, 1962, bayan ya halarci makarantar kwalejin horon soji, wanda ke Kaduna.

Yayin shugabancin kasa daga shekarar 1985 zuwa 1993 inda ya shafe shekaru takwas akan karagar mulkin Najeriya.

Tun bayan rasuwar uwargidansa Maryam Babangida a 2009, tsohon shugaban kasar bai sake yin aure ba sai dai zama da yake yi da ‘ya’yansa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply