Ba Zan Yi Wa Shugabannin Tsaro Ritaya Ba -Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a yayin ganawar shi da manyan hafsun Sojojin Nijeriya makon nan, Shugaban ya ce yana matukar ganin irin jajurcewar su wurin aiki tukuru don ganin tsaro ys tabbata a Nijeriya har ya samu wurin zama.

Bayan haka kuma Shugaban ya ci gaba da cewa Nijeriya Allah ya hore mata shugabannin ojoji masu amana musamman a lokacin gudanar da mulkin mu, don haka maganar ko wani ya ajiye aikin sa duk bai taso ba saboda ire-iren ku Nijeriya take neman a irin wannan lokacin.

Daga bisani shugaba Buhari ya ce kasar nan an dade ana yi wa talakawa mulkin kama karya, tare da danniya na hakkokin su, ciki har da yaudara kan rashin basu tsaro yadda ya kamata.

A karshe dai Shugaban ya kare jawabin nasa da jan kunne ga shugabannin sojin da cewa “ku yi aikin ku domin Allah, ku kuma ci gaba da kare ran al’umma, da kuma dukiyoyin su, sannan kuma ku ci gaba da baiwa sojojin Nijeriya atisaye na kara jarumta domin su ga bayan ta’addanci a wannan kasa tamu”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply