Ba Zan Ta?a Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba – El Rufa’i

Gwamnatin Jihar Kaduna ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Nasir Ahmad El-rufa’i ta musanta labarin da ake ya?awa cewa an na?a wata tawaga da zata jagoranci tattaunawa da ‘yan bindiga a fadin Jihar.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Lahadi.

Ya ce gwamnatin Kaduna ?ar?ashin jagorancin Malam Nasir Ahmad Elrufa’i ta ji labarin ana ya?a jita-jita a kafar sada zumunta cewa gwamnatin ta na?a wakilai da zasu tattauna da yan bindiga a madadinta.

A jawabin da kwamishinan ya yi a madadin gwamnan ya ce: “Gwamnatin Kaduna na kara tabbatar da cewa bata na?a kowa ba dan shiga tsakani da yan bindiga.” Duk Soki Burutsu ne, Bamu na?a kowa dan tattaunawa da yan Bindiga ba, babu sulhu tsakanin mu da ‘yan Bindiga!.

A maganarsa ya ce gwamnatin Kaduna na nan akan bakarta na ba zata tattauna da yan bindiga ba. “Gwamnatin mu ba zata tattauna da yan bindiga ba haka kuma bazata biya kudin fansa ba.

Duk mutumin da aka kama yana haka da sunan wakilin gwamnati za’a hukunta shi kamar yadda doka ta tanazar.” a cewar kwamishinan.A Kwanakin baya dai, Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa gwamnatinsa ba zata tattauna da yan bindiga ba kuma ba zata biya wani ?an bindiga ku?i da sunan ku?in fansa ba.

Related posts

Leave a Comment