Na Yi Bakin Ciki Kan Yadda Matata Ta Karar Min Da Rayuwata Ta Wannan Hanya, Cewar Mutumin Da Matarsa Ta Yanke Masa Azzakari A Garin Tella Dake Gassol, Jihar Taraba
Malam Aliyu Umar ya ce yana tunanin a abinci ko ruwan shan da matarsa ta kawo masa bayan ya dawo daga aiki ta saka kwaya mai sa bacci, wanda hakan ya sa shi nauyin bacci har ta yi nasarar yanke masa gaba.