Ba Zan Iya Zama Dan Majalisa Ba Saboda Ban Da Hakuri – El Rufa’i

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya nuna babu shi babu zuwa majalisar tarayya ta kasa bayan kammala wa’adin Mulki.

An san Gwamnoni da yin takarar Sanata idan sun gama wa’adinsu a jihohi, sai dai anashi ɓangaren Malam Nasir El-Rufai yana cewa ya sha bam-bam da sauran gwamnoni yace bai da hakuri da jajircewar da ake bukata wajen aikin majalisa.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron ‘yan majalisa da cibiyar nazarin aikin majalisa da damukaradiyya watau NILDS ta shirya a Garin Kaduna.

El-Rufai yace aikin majalisa akwai tsauri da wahala tsohon Ministan na birnin tarayya Abuja yake cewa ya san ba zai iya yin aikin da ‘yan majalisa suke yi ba a rayuwarsa.

“Majalisa wani bangaren gwamnati ne da na san ba zan taba iya aiki ba. Hakurin da ba mu da shi, shi ne kokarin samun goyon bayan a goyi-bayan kudirinka. Gudanar da shugabanci a bangaren zartarwa kai-tsaye ne; abin mataki-mataki ne, da zarar kai ne Gwamna a jiha, to shikenan sai yadda ka ce ayi, za ayi. Amma a majlisa, kusan duk daya ake, babu wanda ya fi wani. Hakan ya sa babu jagorancin da yake da wahala kamar ga wadanda kuke duk daya da su.”

“Ba na yi wa shugaban majalisar dattawa ko na wakilai hassada domin kusan aikinsu shi ya fi na kowa wahala a kasar nan. A wajen zartarwa, za ka iya daukar aiki kuma kayi kora. Na san abokan aikinmu Gwamnoni da yawa za su tare a Majalisa. Ina mai tabbatar maku da ba zan taba komawa majalisa ba domin ban tunani zan iya aiki a can.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply