Ba Zan Hana Zanga-Zangar Lumana Ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa ba za ta hana matasa yancinsu na yin zanga-zangar lumana ba, saidai ya gargade su da su yi hattara da wadanda za su iya yin amfani da damar don cimma wata manufarsu ta daban.

Buhari ya faɗi haka ne, lokacin da yake gana wa da Ministan Matasa da wasanni Sunday Dare, ranar Litinin a fadarsa.

Sunday wanda ya gana da yan Jaridar fadar shugaban ƙasa jim kadan bayan kammala ganawar, ya ambato Buhari na shawartar matasan, da su yi hattara da bata gari wadanda za su yi amfani da damar wajen bata kyakkyawar niyyar matasan.

Ministan wanda ya ce ya zo ne don sanar da shugaban ƙasar halin da ake ciki kan masu zanga-zangar EndSARS, ya ce shugaban kasar ya ba matasan tabbacin cewa za a aiwatar da bukatunsu biyar da suka gabatar wa gwamnatin tarayya ta hannun wakilan su.

Zanga zangar wacce yau kwanaki 12 kenan ana gudanar da ita musamman a babban birnin tarayya abuja da jihar lagas ta tsayar da ayyuka da dama. Ko a nan arewacin kasar jaridar muryar yanci ta kawo maku ruhortannin yadda matasan arewacin kasar suke gudanar da zanga zangar kawo karshen ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane inda ko a karshen makon nan anji mai dakin shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari ta goyi bayan matasan arewacin kasar nan kan zanga zangar da sukeyi kan matsalar tsaro da yaiwa yankin arewa daurin demon minti.

A arewacin kasar nan ana iya cewa zanga zangar bai samu karbuwa kamar yadda mutanen kudancin kasar suka fito kan kawo karshen end SARS ba.

A naku tunanin meya janyo hakan? Za muso jin ra’ayoyin ku

Labarai Makamanta

Leave a Reply