Ba Zamu Yi Sake CORONA Ta Yi Mana Illa A Karo Na Biyu Ba – Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya bashi da karfin da zai juri a sake rufe shi a karo na biyu, duba da yadda wasu sabbin rahotanni ke bayyana cewar cutar CORONA zata sake dawowa da ?arfinta a duniya.

A wani jawabi da shugaban kasa, Muhammad Buhari, ya wallafa a shafinsa na tiwita a ranar Alhamis ya ce tattalin arzi?in Najeriya bashi da ?warin da zai iya jure wani sabon kullen. “Duba da irin halin da wasu ?asashe ke ciki, ya zama dole muyi duk yadda za muyi don kaucewa ?ullar annobar COVID-19 a karo na biyu.

“Ya zama wajibi a kanmu mu tabbatar ba mu sake komawa gidan jiya ba.
“Tattalin arzi?in mu bai da ?warin da zai iya jure sake shiga halin da muka shiga na kulle, ba shiga ba fita,” kamar yadda shugaba Buhari ya rubuta.

A watan Maris ne shugaba Buhari ya saka dokar kulle a wasu Jihohi da suka ha?a da Legas, Ogun, da kuma birnin tarayya, Abuja, domin da?ile ya?uwar annobar cutar Korona.

A sakamakon hakan, an samu koma baya a al-amurran tattalin arzi?i, ribar cikin gida da ?asa ke samu (GDP) ta ragu da kaso 6.1% a watanni hu?un farkon shekarar 2020.

Asusun ajiya na ?asar waje shi ma ya ragu da kaso 4.3% a shekarar 2020, wanda hakan ya jawo matsin tattalin arzi?i a karo na biyu cikin shekara biyar.

Related posts

Leave a Comment