Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan yace ko ka?an baza su lamunci abin da ya kira raini ga ‘yan majalisa da wasu jami’an gwamnati ke yi ba.
Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai jim ka?an bayan kammala wata ganawar sirri da suka yi da shugaban ?asa tare da takwaranshi na majalisar dokoki Femi Gbajabiamila a fadar shugaban kasa.
Buhari ya kar?i bakuncinsu ne da yammacin ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2020.
Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Lawan da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, kan hukuncin maaikatar kwadago na ci gaba da shirin daukar maaikata 774,000.
Ya ?ara da cewar ya kamata duk wani jami’in gwamnati musamman ministoci su gane cewar su wakilan shugaban ?asa ne a gaban majalisar, saboda haka ya dace su mu’amalanci majalisar da kyakkyawar mu’amala.
Yan majalisar dokokin tarayyar sun zargi Keyamo da kwace shirin daukar maaikatan daga hukumar daukar maaikata ta kasa, wacce ta samu naira biliyan 52 domin aiwatar da shirin.
Sai dai, Keyamo ya fada wa manema labarai a ranar Talata, cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukace shi da ya ci gaba da shirin daukar maaikatan ba tare da laakari da matsayar majalisar dokoki ba a kan lamarin.
Hakan bai yiwa ‘yan majalisar dadi ba saboda bayan sabanin da suka samu da karamin minista Festus Keyamo, sun bada umurnin dakatar da shirin gaba daya.
Shugabannin sun bayyana ganawar su da Buhari zata haifar da samun maslaha tsakanin majalisar da ?angaren jami’an gwamnati.