Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan yace ko kaɗan baza su lamunci abin da ya kira raini ga ‘yan majalisa da wasu jami’an gwamnati ke yi ba.
Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala wata ganawar sirri da suka yi da shugaban ƙasa tare da takwaranshi na majalisar dokoki Femi Gbajabiamila a fadar shugaban kasa.
Buhari ya karɓi bakuncinsu ne da yammacin ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2020.
Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Lawan da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, kan hukuncin ma’aikatar kwadago na ci gaba da shirin daukar ma’aikata 774,000.
Ya ƙara da cewar ya kamata duk wani jami’in gwamnati musamman ministoci su gane cewar su wakilan shugaban ƙasa ne a gaban majalisar, saboda haka ya dace su mu’amalanci majalisar da kyakkyawar mu’amala.
‘Yan majalisar dokokin tarayyar sun zargi Keyamo da kwace shirin daukar ma’aikatan daga hukumar daukar ma’aikata ta kasa, wacce ta samu naira biliyan 52 domin aiwatar da shirin.
Sai dai, Keyamo ya fada wa manema labarai a ranar Talata, cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukace shi da ya ci gaba da shirin daukar ma’aikatan ba tare da la’akari da matsayar majalisar dokoki ba a kan lamarin.
Hakan bai yiwa ‘yan majalisar dadi ba saboda bayan sabanin da suka samu da karamin minista Festus Keyamo, sun bada umurnin dakatar da shirin gaba daya.
Shugabannin sun bayyana ganawar su da Buhari zata haifar da samun maslaha tsakanin majalisar da ɓangaren jami’an gwamnati.