Ba Za Mu Lamunci Tsagerancin ‘Yan Bindiga – Zulum

Mai girma Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ya zama wajibi Arewa ta tashi tsaye ta dauki matakin da ya dace kan ‘yan bindigan da suka addabi mutane a gidajensu.

Zulum ya bayyana hakan ne a taron kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas karkashin jagorancin sa, wannan shine karo na uku da suka hadu wajen tattaunawar rashin tsaro.

Zulum ya ce dubi ga yadda matsalar rashin tsaro ta tabarbare a Arewa maso yamma irinsu Katsina da Kaduna, akwai bukatar su tashi tsaye kada hakan ya shigo yankinsu.

Ya ce wajibi gwamnonin su tabbatar da aminci ga matafiya a titunan da suka hada jihohin. Dole a kare Jami’o’i da sauran wurare daga hare-haren ‘Yan bindiga, ba zamu yarda ‘yan bindiga suna binmu gida sun sacemu ba.

Kalaman Gwamnan jihar Bornon na zuwa ne a daidai lokacin da ayyukan ‘yan Bindiga ke ƙara ƙamari a yankin Arewa maso yammacin ƙasar, lamarin da ya sanya manya a yankin da suka haɗa da malamai da sarakuna fitowa fili suka ƙalubalanci gwamnatin tarayya da ɗaukar matakan da suka dace.

Labarai Makamanta