Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce daga yanzu majalisar tarraya ba zata kara yarda da raini daga wurin jami’an gwamnati da shugaban kasa ya nada ba.
Lawan ya fadi hakan ne a fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yayin rantsar da kwamitin tuntuba na jam’iyyar APC a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Litinin.
Shugaban majalisar ya bayana cewa kwamitin tuntuba da shugaba Buhari ya rantsar zai inganta sha’anin gudanar da mulki. Ya ce babban makasudin kafa kwamitin shine tabbatar da kyakyawar alaka a tsakanin bangaren majalisa da na zartarwa da kuma bijiro da wasu aiyuka da dukkan ‘yan kasa za su ci moriyarsu.
“Jam’iyya ta fahimci cewa akwai bukatar samun hadin kai da fahimtar juna a tsakanin mambobinta da ke rike da mukamai daban-daban a cikin gwamnati, sannan kuma akwai bukatar tuntuba a kan wasu al’amuran gwamnati da mulki kafin gabatar da su ga jama’ar kasa,” a cewarsa.
Sannan ya cogaba da cewa; “babbar manufarmu ita ce inganta nagartar gwamnati da aiyukan da ta ke yi wa ‘yan Najeriya.
Buhari ya rantsar da kwamitin tuntuba na jam’iyyar APC “Shugaban kasa ya fito karara ya fadi cewa ba zai yarda wani daga cikin hadimansa ya raina majalisa ba. Hakan na tabbata zai kawo karshen matsalar.
Na yi imanin cewa cewa za mu iya aiki tare. “Mu, a bangaren majalisa komai ya wuce, mu na fatan a nan gaba wani mai rike da mukami ba zai raina shugaban kasa ta hanyar raina majalisa ba, majalisa ba za ta jure raini ba a nan gaba.”