Ba Za Mu Lamunci Katsalandan A Babban Zaben Dake Tafe Ba – Buhari

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi alwashin cewa ba zai bari wani mahaluki ya kawo katsalanda ba a zabukan 2023 da ke tafe a fa?in ?asar.

Shugaba Buhari ya ?ara da cewar shugabancin da ba a gina shi kan turbar gaskiya ba, ba zai kawo wa kasa alfanu ba.

Shugaban ?asar ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC da gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya jagoranta a fadarsa da ke Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma ce a karkashin shugabancinsa, zai ci gaba da mutunta ‘yan Najeriya ta hanyar tabbatar da cewa kuri’unsu sun yi tasiri saboda suna da yancin zabar shugabannin da suke so a dukkan matakai.

Related posts

Leave a Comment