Ba Za Mu Lamunci Harin Da Aka Kai Wa ‘Yan Arewa A Abiya Ba – Kungiyoyin Arewa

Wasu kungiyoyin arewacin Najeriya sun bayyana harin da aka kai wa ‘yan arewacin kasar a kasuwar shanu a jihar Abia da ke kudu maso gabashin kasar inda aka kasha mutum takwas, da cewa abu ne da ba za a lamunta da shi ba.

A ranar Talata ne 15 ga watan Fabrairu, 2022 da misalin karfe 11:35 na rana, wasu bata-gari suka dira a kasuwar da ke karanar hukumar Omumauzor, Ukwa ta yamma, inda suka kashe mutum takwas da jikkata wasu da dama da kashe shanu.

Jaridar DailyTrust, ta ruwaito cewa kungiyoyin da suka hada da hadakar Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (Coalition of Northern Groups in Nigeria (CNG) ) da Kungiyar Tuntuba ta Matsan Arewa( Arewa Youth Consultative Forum (AYCF)), a sanarwar da suka fitar daban-daban, sun yi gargadi da cewa hakurin da suke yi ana kashe ‘yan Arewa a Kudu maso gabashin kasar, ya isa haka, ba za su sake yarda da haka ba.

Sun bukaci gwamnatin jihar ta Abiya da ta gaggauta ganowa da kamo wadanda suka yi wannan aika-aika a kuma hukunta su.

Kungiyoyin sun ce suna fatan wannan shi ne zai kasance na karshe, kuma za su zuba ido su ga abin da gwamnatin jihar za ta yi a kai.

Related posts

Leave a Comment