Shugaba Bola Tinubu ya ce ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ba za ta amince da abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar ba.
Da safiyar yau Laraba ne rahotanni suka bayyana cewa dakarun tsaro sun toshe fadar shugaban ƙasa da ofisoshin jami’an gwamnati a kasar.
A martanin da ya mayar a cikin wata sanarwa, Tinubu wanda shi ne Shugaban ECOWAS ya ce ba za a lamunci yunƙurin juyin mulkin sojoji ba.
Sanarwar ta ce “Bayanan da aka samu daga jamhuriyar Nijar na nuni da wasu abubuwa marasa dadi da ke faruwa a ɓangaren shugabannin siyasar ƙasar.”