Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce Afirka ba za ta iya samun ha?in-kai da wadata ba yayin da ‘yan nahiyar ke ci gaba da shiga kunci.A cikin jawabinsa na farko a taron tsakiyar shekara na kungiyar ha?in kan Afrika karo na biyar a Kenya a ranar Lahadi,
Tinubu ya kuma yi garga?in cewa ba za su lamunci cin zarafin ?an nahiyar da ake yi ba kamar kuma yadda ya faru a baya.“Ba za mu iya ha?a kan Afirka ba kuma mu sami wadatar da muke nema yayin da ’yan’uwanmu ke cikin kangin wahala da ba?in ciki. Dole ne mu ci gaba a matsayin nahiya guda da samar da zaman lafiya da wadata.
A cewar wata sanarwa da kakakinsa, Dele Alake ya fitar.Ya kuma bayyana shirin karfafa rundunar ha?in gwiwa ta kungiyar raya tattalin arzikin ?asashen yammacin Afrika domin dakile juyin mulki da yaki da ta’addanci a yankin.