Ba Za Mu Iya Biyan Ma’aikata Cikakken Albashi Ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ta ce ba zata iya cigaba da biyan ma’aikatan Jihar cikakken albashi ba kamar yadda yake a tsare, bisa ga haka ba zai yiwu ta biya ma’aikatan jihar cikakken albashin su na watan Maris ba.

Gwamnatin Kanon ta bakin kwamishinan ya?a labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ya jingina haka da saukar ku?in da suke samu daga gwamnatin tarayya da matsalar tattalin arzikin kasa da ake fuskanta.

Kwamishinan ya kara da cewar kason da gwamnatin jihar ke kar?a daga gwamnatin tarayya ya sauka, wanda bayan nazari akansa suka gano zai yi matu?ar wahala gwamnatin jihar ta iya biyan sabon tsarin albashi.

Sai dai, duk da haka ?ungiyar ?wadago ta jihar (NLC) ta baiwa gwamnatin wa’adin kwanaki bakwai ta maida ma ma’aikatan ragowar albashin su, kamar yadda ya ke a tsare.

Kuma ?ungiyar kwadagon ta bayyana rage ku?in albashin ma’aikatan da gwamnatin ta yi da cewa ya sa?a ma doka. Shugaban kungiyarreshen jihar ne ya bayyana bada wa’adin jim ka?an bayan wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki da ?ungiyar suka yi.

Shugaban ya ce, matu?ar gwamnatin bata dakatar da wannan rage albashin ba har wa’adin ya kare, to ma’aikatan zasu tsunduma yajin aikin garga?i na kwana uku.

Da yake maida martani kan lamarin, kwamishinan ya?a labaran jihar ya ce, shiga yajin aikin bazai warware matsalar ba. Malam Garba ya ce, a watan maris gwamnatin jihar ta kar?i N12,400,000,000 daga asusun gwamnatin tarayya ne.

A cikin wa?annan ku?a?en akwai N6,100,000,000, kason gwamnatin jihar da kuma N6,300,000,000 kason kananan hukumomi 44 da jihar ke da su.

Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnatin jihar na bu?atar ?arin biliyoyin nairori kafin ta iya biyan Albashin ma’aikatan jihar, wanda a yanzun babu ku?in da za’a ?ara ?in.

A cewar kwamishinan, taron da suka yi da ?ungiyar ?wadugon jihar a watan Mayun shekarar data gabata, sun cimma matsayar biyan ma’aikata albashi bisa yadda jihar ta samu daga asusun ?asa.

Ya kuma yi kira ga ?ungiyar ?wadagon da kuma sauran ma’aikatan jihar da su nuna goyon bayansu don cigaba da gina kyakkyawar ala?a tsakaninsu da gwamnati.

Daga ?arshe, kwamishinan ya tabbatarwa da ma’aikatan jihar cewa zasu cigaba da samun cikakken albashinsu da zarar wannan matsalar ta kauce.

Related posts

Leave a Comment