Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Ba Za Mu Iya Biyan ASUU Albashin Aikin Da Ba Su Yi Ba – Gwamnatin Tarayya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin Tarayya ta fa?i dalilin da ya sa ba ta biya mambobin ?ungiyar ASUU ta malaman jami’a cikakken albashinsu na watan Oktoba ba, tana mai cewa ba zai yiwu a biya malaman albasahin aikin da ba su yi ba.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ?auki matakin daina biyan albashin malaman jami’ar na tsawon lokacin da suka ?auka suna yajin aiki tun daga 14 ga watan Fabarairu zuwa 14 ga Oktoba.

Bayan dawowarsu aikin ne kuma gwamnati ta biya su albashin kwana 17, kamar yadda ASUU ke fa?a, kuma ta yi barazanar ?aukar mataki.

Hakan ta sa reshen ?ungiyar na Jami’ar Jos ya umarci malaman jami’ar su yi zamansu a gida, duk da cewa ta ce ba yajin aiki suke yi ba.

Cikin wata sanarwa, mai magana da yawun Ma’aikatar ?wadago, Olajide Oshundun, ya musanta rahotannin da ke cewa gwamnati ba ta yi wa malaman adalci ba.

“An biya su ku?in aikin da suka yi ne kawai a Oktoba, daga ranar da suka soke yajin aiki,” a cewar sanarwar.

“An ?auki matakin ne saboda ba zai yiwu a biya su ku?in aikin da ba su yi ba. Kowa ta kansa yake yi.”

Exit mobile version