Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake jaddada umarninsa ga jami’an taron ?asar da su yi duk mai yiwuwa don ku?utar da ?aliban makarantar Kuriga da ‘yan bindiga suka sace a makon da ya gabata.
Cikin wani jawabi da ministan ya?a labaran ?asar, Mohammed Idris ya yi wa manema labarai, jim ka?an bayan taron majalisar zartarwar ?asar da aka gudanar a fadar gwamnati, ministan ya ce gwamnati ba za ta biya ko sisin kobo ba a matsayin fansa ga maharan don sakin ?aliban.
Ministan ya ce gwamnatin ?asar ba za ta lamunci ci gaba da sace ?alibai don yin garkuwa da su ba, don haka ya ce gwamnati ke kira ga jami’an tsaron da su yi duk abin da ya kamata don tabbatar da sakin ?aliban da sauran mutanen da hannun ‘yan bindiga a fa?in ?asar.
”Idan ta kama gwamnati za ta yi amfani da ?arfin tuwo wajen ku?utar da ?aliban nan, saboda hukumomin tsaronmu a shirye suke ko me za a yi a dawo da wa?anna ?aliban”, in ji shi.
A ranar Alhamis ?in da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantar furamare da ?aramar makarantar sakandiren Kuriga, inda suka sace ?alibai fiye da 280, kodayake gwamnan jihar Uba sani ya ce daga baya wasu 28 sun ku?uta.