Ba Za Mu Biya ASUU Albashin Aikin Da Basu Yi Ba – Ministan Ilimi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar yayin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ke gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jami’o’in ƙasar domin nuna rashin jin daɗinsu game da rashin biyansu albashin watannin da suka kwashe suna yajin aiki, gwamnatin tarayya ta ce ba za ta biya malaman albashin aikin da ba su yi ba.

Ministan ilimin Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Yayin da yake martani game da iƙirarin da shugaban ASUU ya yi na cewa gwamnati na son mayar da malaman jami’ar ma’aikatan wucin-gadi, ministan ya ce gwamnatin ba ta da wannan niyyar.

“An janye yajin aiki, kuma gwamnati ta biyasu haƙƙin iya aikin da suka yi. Ina tunani wannan shi ne matsayin gwamnati, cewa ba wanda za a biya albashin aikin da bai yi ba, sun yi aiki na kwanaki, kuma gwamnati ta biya su haƙƙinsu kwanakin da suka yi”, in ji Adamu Adamu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply