Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi maganarsa ta farko bayan harin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai wa tawagar ma’aikatan gwamnatin jihar ranar Juma’a.
Mun ruwaito muku cewa akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu a harin da yan ta’addan da ake kyautata zato yan kungiyar ISWAP ne suka kaiwa tawagar jami’an gwamnatin jihar Borno yayinda suke hanyar zuwa Baga.
Majiyoyi biyu sun bayyanawa AFP ranar Asabar cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu ya ninku daga Juma’a zuwa yau saboda an tsinci wasu gawawwaki.
Wadanda aka kashe sun hada da ‘yan sanda goma sha biyu, Sojoji biyar, ‘yan sa kai hudu da wasu farin hula tara.Harin ranar Juma’a ne karo na biyu da aka kaiwa gwamnan cikin watanni biyu.
A ranar Asabar a Baga, Zulum ya bayyana cewa tsoron harin ‘yan Boko Haram ba zai hanashi cigaba da aikin da yake yi na mayar da ‘yan gudun hijra muhallansu.
“Ba zan ji tsoron hare-hare ba yayinda nike yiwa al’ummata aiki ba,” inji Zulum