Babban malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, ya yi magana kan kuskuren da gwamnatin tarayya ke yi wajen ceto ɗalibai 287 da malamansu da aka sace a jihar Kaduna.
SheikhGumi ya nuna cewa kuskure ne amfani da ƙarfi wajen ganin an ceto ɗaliban a hannun ƴan bindiga.
Da yake magana a wani shirin gidan talabijin na Arise tv, a ranar Alhamis a Abuja, Gumi ya ce ya kamata gwamnati ta matsa kusa da ƴan bindigan ta yi nazari a kansu domin samar musu da ingantacciyar rayuwa.
A cewarsa, amfani da ƙarfi da gwamnati ke yi yanzu ya mayar da ƴan bindigan sun zama dodanni. A kalamansa: “Waɗannan ƴan bindigan suna ƙara ta’azzara. A baya basu yin haka. Ƴan ƙananan marasa rauni suke farmaka, ƙara ƙarfinsu za mu danganta shi da ƙarfin da ake amfani da shi a kansu.
“Yanzu muna yaƙar ƴan bindiga. Ba a san sunansu ba. Ba za a iya faɗa da wanda ba a sani ba. Mun ce a shiga, a gano su, mu tsara su, mu san su waye da kuma inda suke.
“Duk waɗannan bayanan sirri kusan babu su. Hanyar amfani da ƙarfin da ake bi ita ce ke ƙara tarɓarɓar da lamarin. “Yanzu haka suna garkuwa da yara tare da barazanar kisa, wanda a da ba su yi ba. Don haka, ina tunani abin da ya kamata shi ne a koma a sake lale a daina amfani da ƙarfi.
Ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga yan bindigar akan yadda za a kawo ƙarshen matsalar, ya ce kamata ya yi gwamnati ta tsara wani shiri kamar irin shirin yin afuwa ga tsagerun Neja-Delta da aka yi a baya.
A kalamansa: “Ana buƙatar shiri kamar na Neja-Delta, shirin da zai fitar da su daga dazuzzuka, ilimantar da su, ba su kiwon lafiya, ba su ingantacciyar rayuwa. “A haka ake sanya wa mutane su bar tashin hankali da fitina.