Ba Mu Shirya Komawa Karatu Yanzu Ba – Ɗaliban Jami’ar Bayero

Alamu na nuna cewa da yawa daga cikin ɗaliban jami’ar Bayero dake Birnin Kano BUK ba za su koma karatu a ranar 18 ga Janairu ba kamar yadda hukumar gudanarwar jami’ar ta bayar da sanarwa ba.

Kwana ɗaya da sanarwar janye yajin aiki na tsawon wata tara da ƙungiyar malaman jami’o’in ƙasar nan ta yi, da yawan ɗaliban jami’o’i sun nuna rashin shirinsu na komawa makarantar a lokacin da aka sanar.

“Ban jima da samun gurbin karatu na digiri na biyu a bangare nazari kan sadarwa ba. Amma sam bana tsammanin dalibai sun shiryawa cigaba da karatu haka da wuri.” In ji wani mai suna Al’ameen Usman Abubakar.

Abubakar ya cigaba da cewa; “Kamata ya yi ace hukumar gudanarwar ta kammala yin rijista kafin 18 ga Janairu.”

Ya bukaci jami’ar da ta ƙara lokacin yin rijistar zuwa watan Fabrairu don ɗalibai su samu damar shiryawa kan lokaci da samun zarafin tunkarar karatun.

Ya bukaci jami’ar da ta ƙara lokacin yin rijistar zuwa watan Fabrairu domin sauran ɗalibai su samu damar shiryawa kan lokaci.

Wani ɗalibi mai suna Aminu Muhammad na tsangayar nazarin zamantakewa (Sociology) ya bayyana dalilansa da cewa: “Lahadin da ta wuce ne ma na iya samun shiga shafin yanar gizo na makarantar domin yin rijista wanda har yanzu ake yi.”

Ya cigaba da cewa “Na gama biyan duk wasu kuɗaɗe amma har yanzu ban samu gurbi a jami’ar ba.” Aminu ya yi ƙorafin cewa zai yi wahala ace shi ya samu damar kammala rijistarsa kafin 18 ga Janairu.

Hasiya Abubakar, ɗaliba mai nazarin biochemistry cewa ta yi, “Dawowa karatun nan ya zo mana babu tsammani duk ɗalibai sun gaji da zaman gida.”

Labarai Makamanta