Malamin ya ce sannanen abu ne idan aka ce matsalar tsaro ta ki ci balle cinyewa a arewacin Nijeriya.
Ya kara da cewa da farko mayakan ta’addancin Boko Haram sun addabi yankin Arewa maso gabas, amma yanzu ‘yan bindiga sun gangaro yankin arewa ta yamma da ta tsakiya. Wannan matsalar ta kasance tana ciwa jama’a da dama tuwo a kwarya.
Sheik Adam Albani wanda fitaccen Malami ne wanda lamarin ya matukar saka shi cikin damuwa a wani bidyonsa da ya bayyana, inda yake yi wa shugaba Buhari wankin babban bargo.
A cikin bidiyon wanda ya fara da sautin murya amma daga bisani ya kare da hoto, ya bayyana cewa Shugaba Buhari ba shi da amfani kwata-kwata. .alamin yayi fatan kada Allah ya sake gwadawa ‘yan Nijeriya mulki irin wannan wanda ke cike da tashin hankali.
Malamin yace abin takaici ne a irin wannan halin da al’umma suke ciki wai a fitar da ton 30,000 na masara domin a wadata abincin kaji. To su kuma mutane pa meka tanadar musu?
Sheik Albani ya bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wurin baiwa rayukan jama’a da dukiyoyinsu kariya, domin kuwa wanda hakan yana daga cikin hakkin jama’a a kan gwamnati.