Kamfanin samar da iskar gas na girki a Najeriya, Nigeria LNG Limited (NLNG), ya musanta rahotannin da ke cewa ya dakatar da aiki a wasu masana’antunsa da ke kudancin ?asar saboda ambaliyar ruwa.
Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Twitter, NLNG ya ce dukkan masana’antunsa na aiki “duk da cewa ba yadda suka saba ba saboda ?arancin gas da yake fuskanta daga abokan hul?arsa”.
Tuni aka shiga fargabar hauhawar farashin gas ?in saboda tsoron ?arancinsa a kasuwa bayan kamfanin ya ba da sanarwar rage yawan gas ?in da yake samarwa saboda raguwar da aka samu daga abokan hul?arsa da ke samar masa da ?anyen gas, wanda ambaliyar ta haifar.
“Babu wata masana’antarmu a Tsibirin Bonny ko kuma wani wuri da ta fuskanci matsala sakamakon ambaliyar ruwa,” a cewar kamfanin.
NLNG ya ce yana ci gaba da samar wa kasuwar cikin gida gas ?in daga abin da yake da shi a rumbunsa kuma yana ci gaba da lalubo hanyoyin magance matsalar da ambaliyar ta haifar wa abokan hul?ar tasa.