Ba Mu Da Masaniya Akan Sauya Takardun Kudi – Fadar Shugaban Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ƙasa da sa’o’i arba’in da takwas bayan Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya sanar da cewa bankin zai sauya wasu daga cikin kudaden kasar a ranar 15 ga watan Disamban 2022, gwamnatin tarayya a ranar Juma’a tace bata amince da hakan ba.

Ministan kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed tace bata amince da tsarin ba inda tace in har aka tabbatar da shi za a samu babbar matsala a kasar da tattalin arzikinta.

Zainab wacce tayi tsokaci kan tsarin a yayin martani ga tambayar da Sanata Opeyemi Bamidele yayi yayin kare kasafin kudi na 2023, ta ja kunnen babban bankin kan matsalolin da ka iya tasowa.

Sanata Bamidele wanda a tambayarsa ya sanar da ministan cewa kasa da kwanaki biyu da sanar da tsarin, an fara jin illarsa kan darajar Naira idan aka danganta ta da dala.

“Kwanaki biyu kacal da sanar da tsarin, darajar Naira idan aka danganta ta da dala tayi kasa. Dala daya tana da darajar N740 zuwa N788 sakamakon kokarin da ake wurin ganin an canzata.

“A gani na, wannan tsarin mai kyau ne amma lokacin ne ba daidai ba saboda naira zata iya faduwa har ta kai N1,000 kafin ranar 31 ga watan Janairun 2023 da aka tsayar don tabbatar da tsarin.”

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, yayin amsa tambayarsa, ministan tace bata san da tsarin ba sai dai kawai ta ji shi a kafar sada zumunta ana yamaɗiɗi dashi.

“Masu girma sanatoci, ba a tuntubi ma’aikatar kudi ba kan sake wasu takardun Naira kuma ba zan yi tsokaci kan amfanin hakan ko akasinsa ba. “”Sai dai a matsayinmu na ‘yan Najeriya da suka samu damar kasancewa a matakin sama na fannin, akwai yuwuwar illa mai yawa kan darajar Naira idan ta tabbata.

“Sai dai zan yi kira ga wannan kwamitin da yayi kira ga gwamnan bankin domin samun bayanan da suka dace a fannin amfanin tsarin da daidan shi ko akasin hakan.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply