Shugaban sashin watsa labarai na Kungiyar ‘yan Shi’a mabiya Zakzaky Ibrahim Musa ya nesanta kungiyar da barazanar kisan da jarumin Finafinan kudancin Najeriya Pete Edochie ya ce ana masa saboda fitowa a fim din ‘Fatal Arrogance’ a matsayin Ibrahim El-Zakzaky.
A hirar da Musa ya yi da Alexander Okere wadda The Punch ta ruwaito ya ce kungiyar bata taba yi wa kowa barazana ba tsawon shekaru 40 da kafuwarsu a Najeriya sai dai sune ake kai wa hari.
Ya cigaba da cewa ba su gamsu da dalilan da jarumin ya bayar ba na cewa shi aikinsa kawai ya yi a matsayin jarumi amma ba shi ya rubuta fim din ba.
“A matsayinsa na kwararren jarumi ya kamata ya karanta labarin ya kuma san dalilin yinsa.”
Har wa yau, ya kara da cewa kowa ya lura da irin tufafin da Edoche ya saka a fim din ya san Zakzaky ake kwaikwayo.
Mai magana da yawun ‘yan Shi’an ya yi ikirarin cewa Shugaban Hafsan sojojin kasar Najeriya Laftanar Tukur Buratai ne ya dauki nauyin shirya fim domin sauya abinda ya faru tsakanin sojoji da ‘yan Shi’a a nuna kamar su mutane ne masu son tayar da fitina.
“Ka duba irin tufafin da suka saka kuma suna zanga-zanga suna ambaton ‘Allahu akbar. La ilaha illallah.’ Haka muke zanga-zanga kamar yadda aka sani.”
Da aka masa tambaya ko yana da hujjar cewa Buratai ne ya dauki nauyin yin fim din, ya ce, “Mun san wanda ya rubuta littafin ‘Fatal Attraction’ ka duba yadda ya yi kama da ‘Fatal Arrogance’ kuma dama marubucin mai yi wa sojoji kwangila ne duk cewa suna buya karkashin kungiyoyin jin kai.”
Ibrahim Musa ya ce kungiyar ta nemi kada a fitar da fim din duba da cewa an bata musu suna cikin fim din kuma idan aka fitar za su garzaya kotu su bi hakinsu.