Ba Mu Da Hannu A Ɓacewar Dadiyata – Gwamnatin Jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta zargin cewa akwai hannunta a bacewar dan adawar gwamnati, Abubakar Idris, wanda aka fi sani da ‘Dadiyata’.

Wasu ‘yan ta’adda ne suka dira har gida suka sace Dadiyata, fiye da shekara guda kenan, har yanzu babu labarinsa ko halin da yake ciki.
An saceshi ne a gidansa da yake zaune tare da iyalinsa a unguwar Barnawa da ke cikin garin Kaduna.

Rundunar ‘yan sanda ta sanar da cewa wasu ‘yan ta’adda ne dauke da makamai suka yi awon gaba da Dadiyata yayin da ya dawo gidansa da misalin karfe 1:00 na dare.Tun bayan saceshi, har yanzu ba a ga Dadiyata ko motarsa kirar BMW da aka tafi da shi a cikintaba.

” A cikin wani jawabi da kwamishiniyar Shari’a a jihar Kaduna, Aisha Dikko, ta fitar ranar Litinin, gwamnatin Kaduna ta ce bata da masaniyar inda Dadiyata ya ke.

“Ma’aikatar Shari’a ta jihar Kaduna ta na mai sanar da cewa gwamnatin Kaduna ba ta da hannu ko masaniyar inda Abubakar Idris Usman (Dadiyata) ya ke tun bayan samun rahoton saceshi.”Duk wanna abu da ake yadawa sabanin hakan sharri ne kawai domin batawa gwamnati Kadunan suna saboda kawai a garin Kaduna aka sace shi.

“Ita gwamnatin Kaduna kotu ta ke kai duk wani mutum da take zargin ya yi mata karya, kazafi ko kage domin ya girbi abinda ya shuka,” a cewarta.Dadiyata ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Labarai Makamanta

Leave a Reply