Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce lallai gwamnatin jihar bata biya komai ba a matsayin kudin fansa don sakin daliban makarantar sakandare na kimiyya da ke Kankara ba.
Mustapha Inuwa ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Talata a Katsina, cewa koda dai an wahala sosai wajen ceto yaran daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su, ba a biya ko sisi a matsayin kudin fansa ba.
Ya ce gwamnatin jihar ta yi amfani da dabaru da dama wajen sakin yaran cewa “a yayin aikata hakan, mun tabbatar da ganin cewar ba a rasa kowane rai ba.”
Sakataren gwamnatin ya ce: “sabanin rade-radin da ake yi a wasu bangarori cewa gwamnati ta biya naira miliyan daya don ceto kowane dalibi guda, gwamnatin bata biya ko sisi ba. “Koda dai, tsarin ya kasance mai tsananin wahala, mun tabbatar da ganin cewa ba a rasa rai ba a yayin aiyukan, muna farin ciki cewa sun dawo cikin koshin lafiya sannan sun sake saduwa da iyayensu.”
Ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya da ta fuskacin amfani da ‘yan sanda da sauran hukumin tsaro wajen tabbatar da sakin yaran ba tare da ko ƙwarzane ba.
A ranar 11 ga watan Disamban 2020 ne wasu ‘yan bindiga bisa Babura ɗauke da manyan Bindigogi suka yi garkuwa da dalibai 344 daga makarantar sakandare na kimiyya da ke garin Kankara a jihar Katsina.