Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya ta bayyana cewar ko ka?an babu adalci a kamun da akayi wa Sanata Ndume sakamakon tsaya wa Maina da ya yi, sannan a hannu guda a bar wanda ya tsayawa Nnamdi Kanu Sanata Abaribe yana watayawa.
A cikin wata takardar sanarwa da Matasan suka fitar wadda ta samu sanya hannun shugaban ?ungiyar Alhaji Yerima Shettima, sun bayyana cewar abin takaici ne da Allah wadai wannan mataki da Kotu ta ?auka, kuma ba abu ne wanda za’a lamunta ba, doka ta yi aiki akan wani ?angare ta kuma yi ?ememe a ?ayan ?angaren.
Matasan na Arewa sun bu?aci cikin gaggawa Kotu ta bada umarnin kamo Sanata Abaribe wanda ya tsayawa ?an ta’adda Nnamdi Kanu shima a gar?ame shi a kurkuku har sai idan Kanu ya gabatar da kanshi.
“Dukkanin su su biyun Ndume da Abaribe Sanatoci ne a majalisar ?asa, babu wani banbanci na fifiko da Abaribe yake da shi akan Ndume, sai dai in kawai domin ?aya ya fito daga Arewa ne shi kuma dayan daga Kudu, to muna bukatar sani”.
Muna kira da babbar murya ga shugaban ?asa Buhari da ya shigo cikin lamarin ya zamana adalci ya tabbata a tsakanin Sanatocin ba tare da nuna wani banbanci ba.