Ba Gaskiya Bane Labarin Cewa Mun Kama Magu-DSS

Hukumar jami’an tsaro na farin kaya (DSS) ta ce ba ta kama mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ba.

A cikin wata sanarwa da jami’an hulda da jama’a, Peter Afunanya, DSS ta ce babu gaskiya a cikin labarin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa a kan cewa ta kama Magu.

“Hukumar DSS ta na son sanar da jama’a cewa ba ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFFC, ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka bayyana ba.

“DSS ta fitar da wannan sanarwa ne a yammacin Litinin, 6 ga watan Yuli, bayan yawan tuntubarta a kan zargin kama Magu,” a cewar sanarwar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply