Ba Gaskiya Ba Ne Cewar An Kama Ni – Rahama Sadau

Fitacciyar Jaruma a masana’artar Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta ce babu wanda ya kamata sannan babu wanda ya yanke mata hukunci a gidan yari,

Jarumar ta bayyayana a shafinta na Tweeter bayan da bayanai yake ta yaduwa a kafafen sada zumunta cewa an kamata kuma an gurfanar da ita a Gaban kotun shariar Musulunci, kan zargin batancin da aka yi fiyayyen halitta Muhammad SAW, ta ce bata da masaniya da inda labarin ya samo asali, don haka ta yi kira ga mutane da su daina yada labarin Karya marasa makama,

A makon da ya gabata ne dai Rahama Sadau ta wallafa Bidiyon a tweeter da ke nuna bayanta a bude inda mutane sukaita rubdugu da tofin Allahtsine duk da wasu na caccakar jarumar wasu kuma na kareta.

Sai dai mafi yawan wadanda suka fito daga kudu suna yabon jarumar ne, yayin da wadanda suka fito daga arewacin Nigeriya suke sukarsa, inda wani ya yi batanci ga manzo SAW a kasan hotunan lamarin da ya jawo cece kuce musamman daga arewacin Nigeriya.

Related posts

Leave a Comment