Ba Fulani Suka Kai Hari Sakandaren Jihar Kogi Ba – Gwamnati

Gwamnatin jihar Kogi ta karyata rahotannin da ke cewa makiyaya Fulani ne suka kona makarantar sakandare ta Illuke Bunu inda ta ce kona daji ba bisa ka’ida bane ya janyo gobarar, saɓanin labaran da wasu ke yaɗawa na cewar harin Fulani ne.

Hakan ne kunshe ne cikin sanarwar da kwamishinan watsa labarai na jihar, Mista Kingsley Fanwo ya fitar mai taken, ‘Rahoton farko game da kona makarantar sakandare ta Iluke Bunu.’ Ba makiyaya bane suka bankawa makarantar sakandare wuta.

Sanarwar ta kuma ce gwamnatin za ta cigaba da zurfafa bincike yayin da ta yi tir da wadanda ke gaggawar alakanta lamarin da wani sashi na al’umma.

“Konewar makarantar sakandare ta Iluke Bunu abu ne da gwamnati ta damu da shi. “Gwamnatin jihar tana tir da gaggawan da wasu suka yi na cewa makiyaya Fulani ne suka kona wani sashi na makarantar.

Irin wannan rahoton mara tabbas na iya tada tarzoma a jihar. “Binciken da muka fara gudanarwa ya nuna cewa kona daji ba bisa ka’ida ba da wasu mutane biyu da ba a gano su ba suke yi ne ya janyo gobarar.

“A yayin da muke cigaba da bincike kan sababin gobarar, muna gargadi game da yin kalaman da za su iya kawo cikas ga zaman lafiyar da ake yi tsakanin kabilu a jihar Kogi.

“Al’ummar Kogi suna zaman lafiya da Fulani, Bassa, Nupawa da sauran mutane da ke zaune ko yin kasuwanci a jihar,” a cewar wani sashi na sanarwar.

Shugaban karamar hukumar Kabba/Bunu da mai bada shawarar kan tsaro na jihar sun bukaci hukumomin tsaro su binciko wadanda suka aikata abin don fuskantar sharia.

Labarai Makamanta

Leave a Reply